ABOUT THIS EPISODE
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan murabus ɗin da shugaban hukumar kwallon ƙafa ta Najeriya NFF Alhaji Ibrahim Gusau da wasu daga cikin mambobin kwamitin zartarwarsa suka yi, bayan matsin lambar da suka fuskanta kan koma bayan da tawagogin ƙasar suka samu a manyan gasanni na duniya, ciki har da gaza samun gurbin da tawagar mata ta ƙasar ta yi a gasar lashe kofin duniya da za a yi a shekara mai zuwa.
A cewar rahotanni, 8 daga cikin mambobin kwamitin 13 ne suka yi murabus daga jagorancin hukumar ta NFF, lamarin da ya haifar da shakku gameda zaɓen shugabannin hukumar da za a yi nan ba da jimaba.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............
Hausa
Niger
OTHER EPISODES IN THIS PODCAST
Shirin Duniyar Wasanni na yau ya mayar da hankali kan dambarwar da ta kunno kai a sashen wasanni na Najeriya bayan da hukumar wasannin ƙasar ta baiwa mambobin kwamitin ƙolin NFF wa’adin sa’o’i 24 tun a juma’ar da ta gabata kan su ajje aiki.
Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da…
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya mayar da hankali kan wasannin gab da na kusa da ƙarshe na gasar cin kofin duniya da aka kammala tsakanin ƙasashe 8 wanda kuma kawo yanzu ya rage ƙasashe 4 a wannan tafiya wadda ta faro da ƙasashe 48.
A wasannin dai Faransa ta yi waje da …
Shirin Duniyar wasanni a wannan makon tare da Khamis Saleh ya yi duba ne a gameda nasarar da tawagar Spain ta yi kan takwararta ta Argentina a gasar cin kofin duniya karo na 23
Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.........
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Shamsiyya Haruna ya yi duba ne kan irin koma bayan da ake gani na faruwa a tsakanin tawagogin kwallon kafar Najeriya, kama daga bangaren mata mata da maza, har ma da yan wasa masu tasowa.
Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda ba a samun sabbin ƙasashen da ke lashe gasar kofin duniya.
Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Disclaimer: The podcast and artwork embedded on this page are from RFI Hausa, which is the property of its owner and not affiliated with or endorsed by Listen Notes, Inc.
EDIT
Thank you for helping to keep the podcast database up to date.